Maganin Shawara: Likita ta gargadi iyaye mata a kan disa ruwan nono a idon jarirai

Posted by Jenniffer Sheldon on Monday, September 16, 2024

- Likitar yara a babban asibitin Lagas ta magantu a kan wasu sakaci da ake yi ta bangaren kula da lafiyar jarirai

- Dr. Ademolu Abiola ta gargadi iyaye mata a kan diga ruwan nono cikin idanun jarirai da sunan maganin shawara

- Ta bayyana cewa ganyen gwanda, maganin kashe kwayoyin cuta ta 'ampiclox' da ruwan nono duk basa maganin shawara

Wata likitar yara a babban asibitin Ikorodu, jihar Lagas, Dr. Ademolu Abiola, ta yi gargadi a kan matsa ruwan nono a idanun jarirai da sunan maganin shawara.

Dr. Abiola, wacca tayi gargadin a yayin wata hira da jaridar Punch HealthWise, ta kuma yi gargadi a kan amfani da ruwan gwanda da maganin ampiclox a kan yara masu fama da wannan lalura ta shawara.

Cutar shawara da bature ke kira da ‘Jaundice’ta kan sauya kalar fatar jikin yara saboda kari da aka samu na‘bilirubin’ a jini.

A cewar kungiyar lafiya ta duniya, cutar shawara na daya daga cikin manyan alamu na bayyane da ake lura da su a tattare da jariri.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Zaben cike gurbi: APC ta lashe kujerar Sanata a Plateau ta kudu

Abiola ta ce mafi akasarin cutar shawarar jarirai abune da sai an yi nazari a kai, inda yayigargadin cewa yana da matukar muhimmanic a dunga kula da lamarin domin hana shi tabarbarewa.

“A matsayinmu na likitoci, muna sane da abubuwa da dama da ke faruwa a waje, musamman wajen kula da sabbin haihuwa.

“A matsayinmu na likitocin yara, mun san cewa yara kan samu matsaloli a wasu lokutan idan aka haife su; amma ba batun rashin lafiyar yara bane idan aka haife su illa batun kulawa da wasu lamura da ke da muhimmanci a wajenmu.

“Akwai wasu dabaru na gida da ke da illa ga kananan yara, kamar idan aka baiwa yara maganin kashe kwayoyin cuta ta ampiclox a matsayin maganin shawara. A wasu lokutan ma, wasu mata kan disa ruwan nono a idanun yara.

“Tabbass, a matsayin masana cututtukan shawara, zai bar garkuwar jiki. Bai da wani alaka da disa ruwan nono a idanun jariri ko amfani da ampiclox,” in ji ta.

Abiola ta ce cutar shawara na iya zama mara hatsari ko mai hatsari.

“Mafi akasarin jarirai na da shawara mara illa, amma wanda bai da ilimi kana bun ba zai gane banbancin ba sannan wannan ne dalilin da yasa idan ga kula da launin idon yaron ya zama launin dorawa, sai a garzaya da shi cibiyar kiwon lafiya mai kyau domin likitan yara ya duba shi.

“Don haka, amfani da ruwan nono ko ampiclox baya yiwa yara maganin shawara.

“Cutar shawara mara illai zai tafi da kansa. Wato ma’ana imma kayi magani ko kada kayi zai tafi.

“Sai dai kuma, kada kayi sakaci saboda baka san ko mai illa bane ko mara illa, musamman a matsayinka na wanda bai da ilimin abun,” in ji ta.

Ta kara da cewa mutum na iya zaton shawara mai illa a cikin sa’o’i 24 na farko bayan haihuwa.

“Jinirin da aka haifa yau-yau na iya kamuwa da cutar shawara sannan idan ka lura da shawara a ranar farko na rayuwa, ana kiran shi da mai illa kuma a ka’ida, bai kamata ace jinjiri ya samu shawara ba cikin sa’o’i 24, don haka idan ka lura da hakan cikin sa’o’i 24, toh mai illa ne.

“Irin wannan cuta ta shawara na bukatar kulawar gaggawa kuma ya zama dole a dauki mataki cikin sauri domin yana iya kaiwa ga lalacewar kwakwalwa.

“Abu mafi kyawu ko mafita shine da zaran ka lura da launin dorawa a idanun yara, sai kai su domin likita ya duba su; sannan daya daga cikin hanyoyi mafi inganci shine daukar sumfuri da kuma aikawa dakin gwaji.

KU KARANTA KUMA: Zaben cike gurbi na Cross River: Yar takarar PDP Akwaji ta lallasa na APC

“Amfani da ruwan gwanda, ampiclox, da ruwan nono ba magani bane.

“Akwai wani jinjiri da aka kwantar a nan, mahaifiyarsa ta kais hi asibitin kudi, inda aka daura jinjirin kan magungunan kashe kwayoyin cutar sannan jinjirin ya mutu saboda abun ya tabarbare.

“Abu mafi inganci da ya kamat mutum yayi shine daukar jinjirin zuwa wajen likitan yara ko kuma wani likita mai inganci da ya san kan cutar,” ta jaddada.

A gefe guda, Farfesa Ali Muhammad na sashen koyar da ilimin kasuwanci a jami'ar BUK ya rasu, kamar yadda Legit.ng Hausa ta tabbatar.

A ranar Juma'a, 4 ga watan Disamba, ne Farfesa Ali ya wallafa cewa ya na neman jama'a su taya shi da addu'a saboda an kwantar da shi a asibiti.

Bayan ya yi sallama irinta addinin Musulunci a shafinsa na Facebook, Farfesa Ali ya yi wasu zantuka.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHB9knJnamlhYrqis8CnoKdlo52uuK3RmmSloZuewaJ505pkoJminK6ltYyisJqxlWK6osDAZphmo5GjeqW10ppkq62nlrtuus6npmaZXZ6xsLqMo5iroaKWtm%2B006aj